Shugaban kungiyar NANS, Usman Barambu, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce zanga-zangar da za ta fara ranar Litinin, za ta kasance har sai Mohammed ya sami ‘yanci.
A baya dai kungiyar ta nemi gafarar uwargidan shugaban kasar yayin da ta kuma yi kira da a sako dalibin.
“Sakamakon gazawar da muka samu wajen neman ‘yancin daya daga cikin mu da aka kama ta hanyar razanawa, azabtarwa, cin zarafi, da tsare shi da jami’an gwamnati suka yi, muna sanar da matakin da shugabannin suka dauka na ci gaba da zanga-zanga a fadin kasar,” in ji sanarwar.
“Mun yi kokarin tuntuba kuma mun nemi afuwa, amma hakan ya gaza haifar da kyakkyawan sakamako wajen neman ‘yancin Mohammed, don haka za a fara zanga-zangar kamar haka: Litinin, 5 ga Disamba, 2022 a duk fadin kasar.
Rahotanni sun ce jami’an tsaro ne suka dauke Mohammed, bayan sun bibiye shi zuwa Jigawa tare da tafiya da shi Abuja a watan Nuwamba.
A ranar Laraba ne, mai shari’a Halilu Yusuf na babbar kotun birnin tarayya ta gurfanar da Mohammed tare da aikewa da shi gidan yarin Suleja a jihar Neja bisa zargin bata sunan uwargidan shugaban kasa.
Kama Adamu ya haifar da martani a shafukan sada zumunta, inda fitattun ‘yan Najeriya suka yi kira da a sake shi, yayin da Aisha Buhari ke ci gaba da fuskantar suka.
Barambu ya lura cewa zanga-zangar ta NANS za a yi ta ne bisa adawa da matakinuwargidan shugaban kasa da kuma babban sufeton ‘yan sanda, Usman Baba.