Daga Walid Y Hari
Wata kotun majistare da ke zamanta Kano karkashin Mai Shari’a Mustapha Datti, ta ba da umarnin daure wani saurayi mai kimanin shekaru 27, a gidan gyaran hali kan zargin zamba da sabawa sassa na 322 da 312 na kundin dokoki Jihar Kano.
An shaida wa kotun cewa matashin wanda mazaunin unguwar Hotoro Danmarke ya yaudari mutum 10 wajen karbar kudadensu da suka kai kimanin miliyan 30.
Lauyoyin masu kara, wadanda ke karkashin jagorancin Sulaiman Sale, sun bayyana sun ce wanda ake zargin ya karbi kudadensu da zummar yin kasuwancin shaddoji da atamfofi bisa alkawarin zai dawo da kudi da riba. Bayan ya karbi kudaden, a cewar lauyoyin, sai ya saba alkawarin.