Sabon shugaban Kenya na shirin cire tallafin man fetur.
Daga Walid Y Hari.
A rana ta farko da ya shiga ofis, Shugaban Kenya William Ruto ya soke wasu shirye-shiryen gwamnatin wanda ya gada, wato Uhuru Kenyatta.
Shugaba Ruto ya kuma nada alkalai shida da Hukumar kula da Ayyukan Shari’a ta tantance shekaru uku da suka wuce, wadanda Mr Kenyatta ya ki nadawa bisa zargin cewa gurbatattu ne.
Za a rantsar da da alkalan a ranar Laraba.
Sabon shugaban ya kuma yi kalaman da ke nuna cewa zai iya soke tallafin abinci da na man fetur.
A cewarsa ana kashe makudan kudi kansu kuma ba a moriyarsu yadda ya kamata.
Mr Ruto kazalika ya ce daga yanzu ba za a kara tantance kwantenoni idan ba a tashar Mombasa ba, wanda a gwamnatin baya ana aikin tantancewar a tashar Naivasha.
Da ma matakan da Mr Ruto ya fara dauka na daga cikin alkawuran da ya dauka lokacin kamfe.