Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a Abuja wadda mai sharia Nkeonye Maha, yake jagoranta ta goyi bayan cigaba da garkame jagoran masu garkuwa da mutane Tukur Manu na tsawon kwanaki 60 da hukumar DSS tace zatayi.
Tun a ranar 12-09-2022 hukumar DSS ta garzaya gaban kotun tarayya tare da neman kotun ta amince mata cigaba da tsare Tukur Mamu har zuwa lokacin da za ta kammala binciken da take aiwatarwa.
Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa an kama Mamu ne tun a Ranar 6-09-2022 birnin Kayro na kasar Masar inda yake kokarin wucewa kasar Saudi Arabia
Bayan kama shi hukumar DSS taja kunnen yan Najeriya kan tofa albarkacin bakinsu har sai ta kammala bincike