An gano cewa matashi mai suna Ebimotimi da cincirindon wasu matasa suka yi wa dukan kawo wuƙa har ya zama ajalisa, bisa zargin ya saci burodi, yana da taɓin hankali.
Wasu ƴan’uwa da maƙwabta na Ebimotimi Freeborn Opuofoni ne suka tabbatar da hakan.
Kafar sadarwa ta BBC ta ruwaito cewa, ba ma burodi ya sata ba, ƙullin Madiga ne, wani nau’in abinci na filawa da ake yin sa a wani yanki na jihar Bayelsa.
Madiga dai wani abinci ne da gidajen burodin yankin suke yi mai kama da burodi, sai dai ya fi tauri kuma yara da manya suna cin sa da bota ko kuma su ci shi gaya.