Dangin A.A Rufa’i da ake ta yada bidiyonsa a kafafen sadarwa da sunan nishadi sun ce za su soma daukar matakin shari’a ga masu yin hakan.
Dangin sun bayyana hakan ne a Yayin ziyarar da suka kai gidan Rediyon Dala FM da ke birnin Kano tare da A A Rufa’i.
Kazalika sun yi bayani a kan rashin lafiyar da A A Rufa’i yake fama da ita, da kuma irin kokarin da suke yi wajen nema masa magani.
A karshe sun bukaci masu son taimaka masa don ya samu lafiya su tuntube su bawai su rika yamadidi da shi ba.
Kana sun ce kofa a bude take don taimaka masa