Ƙasar kenya ta jajirce wajen gudanar da zanga-zangar adawa kan tsadar rayuwa da ƙarin haraji, lamarin da ya rikiɗe zuwa tashin hankali, inda aka kashe akalla mutum 24 a ƴan watannin nan.
A lokacin zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a bara, James Wainaina, direban tasi a Nairabo babban birnin ƙasar, ya zaɓi William Ruto, wanda ya bayyana kansa a matsayin ɗan takarar abin da ya kira ‘ƙasar da take fafutika da harkar tattalin arziki’.
Amma yanzu Mista Wainaina yana jin an ci amanarsa kuma yana goyon bayan zanga-zangar.
BBC hausa ta ruwaito cewa tun lokacin da shugaba Ruto ya hau karagar mulki, farashin kayayyaki ke ci gaba da hauhawa yayin da kuma gwamnatinsa ta ƙara haraji.