Daga DANTALA UBA NUHU KURA
Kwamitin samar da tsaro da Cigaban Garin Ciromawa dake Karamar Hukumar Garun-Malam Sunyi Nasarar Kama Wani Matashi Mai-Suna Dayyabu Shuaibu Ciromawa Cikin Dare Da Suke Zarginsa Da Satar Babur Wanda yakai Kimar Kudi Kimamin Naira 450,000
Bayan Kama wannan Dantahaliki yan kwamitin sun Danka Shi Ga Jamian Tsaron Yan-Sanda Na Karamar Hukumar Garun Malam inda tuni Suka Gurfanar Dashi a Gaban Kotun Shariar Musuluncin Ta karamar hukumar Kura, wadda Maisharia Malam Ibrahim Isa Usman yake jagoranta.
Bayan Maigabatar Da Kara Insifecta Maaji Ya Karanta Masa Takardar Tuhuma Nan Take Ya Musanta Zargin da Cewa Shi Bai Aikataba wannan laifi ba.
Mai-Sharia Malam Ibrahim Isa Usman Ya Waiwayi Maigabatar Da Kara Insifecta Maaji Yace Kaji Ya Musanta
Sai Maigabatar Da Kara Yace Dama Suma Basu Kammala gudanar Bincikeba Ya Kuma Roki Kotu Da Ta Sake Sanya Rana Inda a Yanzu Haka Kotu Ta Sanya Rana Sai Ra 18/10/2022 domin Cigaba Da Shariar
Kuma nan take Maisharia ya Damka shi a Hanun Jamiin Gidan Ajiya Da Gyaran Hali Insifecta Muhammd Baayi Maka Wargrave domin Kaishi Sabon Matsagunin sa na Gidan Ajiya Da Gyaran Hali.
Insert is available in this contact 08131189284