Kotu ta hukunta wani matashi ta hanyar yi masa bulala 10

Wani matashi mai Muhammad Inuwa ya rabauta da bulala daidai har guda 10 sakamakon kamashi da laifin yin guzurin tabar wiwi ga abokan sa.

Tun da fari matashin ya tara abokan sane da zummar zasu je su taya shi aikin gonar sa inda yayi musu alkawarin zai tafi musu da guzurin da zai kara musu karsashi yayin da suke gudanar da aiki a gonar tasa.

Hakan ce tasa Inuwa baiyi wata wata ba yagansa dacewar tanadar tabar wiwi domin kansa da abokan nasa.

Sai dai Bayan ya yi kayan waccen tabar ta wiwi ne kuma ya dauki hanyar sa ta zuwa gonar tasa da abokan nasa suke taya shi aiki sai yayi kacibis da jami’an tsaro sukuwa sukace da wa Allah ya hada mu

Nan Take suka fara gudanar da bincike kan wannan Dan tahaliki inda suka samu tabar wiwi sinki-sinki a tare da wannan bawan Allah.

Bayan kammala binciken nasu ne basu yi wata-wata ba suka gurfanar da shi a gaban kotun Shariar Musulunci ta Karamar Hukumar Kura wadda Maisharia Malam Ibrahim Isa Usman Yake jagoranta.

Nan take mai sharia bayyi wata wata ba yaga dacewar hukunta Inuwa ta hanyar bayar da umarnin a yi masa bulala har guda 10 kuma a kava aiwatar da hukuncin nan take.

Insert is available in this contact 08131189284

 

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments