Wata kotun majistare a jihar Adamawa ta sanya ranar 15 ga watan Yuli domin ci gaba da sauron ƙarar da aka shigar a gabanta bisa tuhumar da ake yi wa wasu mutane huɗu a kan kisan wani mutum kan zargin maita a wani gari da ke karamar hukumar Guyuk.
Rundunar yan sanda Kaduna kasa reshen jihar Adamawa ta ce duk da cewa ta gurfanar da mutanen a gaban kotu amma har yanzu tana cigaba da bincike kan al’amarin.
Ana tuhumar mutanen huɗu da kashe tare da ƙona wani mutum da ake kira Benson Tomothy mai shekara 57 a garin Dumbun Dutse da ke karamar hukumar Guyuk.
Ta ce mutanen sun kashe Benson ne sakamakon zargin maita da ake yi masa, kuma suna zarginsa da hannu a mutuwar yara ƙanana a garin na Dumbun Dutse.
SP Sulaiman Yahaya Nnguroje shi ne kakaki rundunar ƴan sandan jihar Adamawa kuma ya yi ƙarin bayani inda ya ce: “Mun samu labarin sirri da ya faru ranar 15 ga watan Mayun 2022 cewa wasu mutum hudu suka yi hadaka suka kashe Benson bisa tuhumarsa da maita.
“Abin ya faru ne bayan wata hatsaniya tsakanin Benson din da wani Ezekiel bayan sun sha giya sun bugu sai suka fara jifan juna da zargin maita, hakan ne ya jawo rikicin da har waɗancan suka taru suka kashe shi.
“Hakan ne ya sa kwamishinan ƴan sandan jihar Adamawa ya bayar da umarnin a gaggauta kama su, kuma aka gurfanar da su gaban kotu don yi musu hukuncin da ya dace.”
Bayanai sun ce alamarin ya faru ne a wata mashaya da ke garin na Dumbun Dutse inda ake zargin cewa mutanen sun yi masa duka da sanduna tare da jifansa da duwatsu kafin daga bisani suka ƙona shi.
Haka kuma masu gabatar da ƙara na zarginsu da haɗa baki domin aiwatar da kisan kai sun yi zargin cewa mutanen huɗu sun haɗa baki ne domin su kai wa mamacin hari.
Sai dai rundunar ƴan sandan jihar Adamawa ta ce duk da cewa ta gurfanar da mutanen gaban kotu amma har yanzu tana cigaba da gudanar da bincike a kan al’amarin kamar yadda kakakinta SP Nnguroje ya bayyana.
“Sakamakon bincike ya nuna an samu wau mace-macen sai dai babu hujja, don haka ana ci gaba da tattara bayanai don ƙara gano waɗanda ke da hannu a ciki.”
Masu gabatar da ƙara na zargin mutanen da haɗa baki domin aiwatar da kisan kai, sai dai dukkaninsu sun musanta zargin.
Amma alkalin kotun ya bayar da umarinin a cigaba da tsare su a gidan kaso.