Jagoran kuma madugun Jam’iyyar APC kana daya daga cikin na gaba-gaba wajen neman tikitinb tsayawa takarar shugaban kasa mai zuwa Bola Ahmed Tinubu, yace in da ba don goyan bayan da ya baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba, da ya fadi zaben shekarar 2015.
Yayin da yake jawabi ga tawagar ‚yayan Jam’iyyar APC a Abeokuta dake Jihar Ogun, gabanin zaben fidda gwanin da za’ayi a karshen wannan mako, Tinubu ya bayyana cewar shi kadai ya zabi mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a matsayin wanda zai marawa Buhari baya.
Jagoran APC yace ya zama wajibi a karon farko ya bayyana abinda ya faru a Jihar Ogun wadda itace mahaifar Osinbajo wanda yanzu haka yake fafatawa da shi wajen ganin Jam’iyyar APC ta tsayar da shi takarar shugaban kasa.
Tinubu yace Buhari ya bashi damar tsayawa mataimakin shugaban kasa, amma wasu bangarori a Jam’iyyar suka yi tsaye cewar haka ba zai yiwu ba saboda dukkansu Musulmai ne, abinda ya sa aka bukaci ya gabatar da sunayen mutane 3 domin samun kujerar.
Tsohon gwamnan Lagos yace a lokacin ya rubuta sunayen mutane 3 da suka hada da Yemi Kadoso da Wale Edun da kuma Yemi Osinbajo, kafin daga bisani ya yanke hukuncin gabatar da sunan Osinbajo.
Tinubu yace daga nan suka shiga fafutukar ganin Buhari ya samu nasara, ganin cewar sau 3 yana takara amma baya samun nasara, kamar yadda shi da kan sa ya fada.
Jagoran yace da kan say a tashi zuwa Katsina inda ya gana da Buhari, ya kuma shaida masa cewar kaad yayi wasa da batutuwan da suka shafi Yarbawa, kuma tun da ya hau, ba’a nada shi (Tinubu) minister ba, kuma bai karbi kwangila ba.
Tinubu yace yanzu lokaci yayi da Bayeribe zai zaam shugaban kasa, kuma lokacin shi ne.