Inuwar kungiyoyi da ta tara sama da kungiyoyi 140 a fadin Nageriya dake fafutuka wajen kare hakkokin Bil’adama sun aike da rubutaccen sako zuwa ga Alkalin Alkalai na jihar Kano bisa Jan kafa da tace kotu na yi a kan Shariar Dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Tudunwada da Doguwa, Alasan Ado Doguwa
Doguwa ana zargin sa ne da laifuka da suka hadar da tayar da hargitsi yayin fadar sakamakon zabe da kisan kai da kuma kone kone
Kungiyoyin masu fafutukar ganin an tsaftace siyasa an Sami nagartaccen shugabanci a Kano da fadin kasa Nageriya sun ce sun damu matuka da yadda bangaren sharia ya ke Jan kafa a tuhume tuhume da ake yiwa wadanda ake zargi musamman honorable Alasan Ado Doguwa