An buƙaci Majalisar Dattawa ta yi watsi da sunan Stella Okotete, ɗaya daga cikin waɗanda Tinubu zai naɗa ministoci
Wani lauya mazaunin Abuja, Oladotun Hassan ne ya miƙa wannan buƙata bisa zarginta da ya yi da cin hanci da rashawa
Okotete dai ɗaya ce daga cikin mutane 28 da Shugaba Tinubu ya aika da sunayensu Majalisar Dattawa domin a tantancesu
Hassan ya bukaci a gudanar da sahihin bincike kan badaƙaloli na maƙudan kuɗaɗe da ya zargi Stella da aikatawa a bankin na Nexim.
Ya zargeta da amfani da matsayin na wajen damfarar bankin biliyoyin naira da daloli ta hanyar amfani da sunayen wasu kamfanoni na ƙarya.