Bayan juyin mulki shugaban kasar Niger ya nemi al’umma su bashi hadin kai

An ayyana Janar Abdurahamane Tchiani a matsayin sabon shugaban Jamhuriyar Nijar, bayan tuntsurar da gwamnatin tsohon shugaban ƙasar Mohamed Bazoum.

Tchaikovsky ya bayyana a kafar yada labarai ta talabijin ta ƙasar, inda ya zayyano matsalolin da ya ce ƙasar na fuskanta da suka kai su ga ɗaukan matakin kifar da gwamnatin Bazoum

Daga baya Janar Tchiani ya yi kira ga al’umma ƙasar su bai wa gwamnatin sa haɗin kai ta yadda za a samu nasarar tafiyar da lamurran ƙasar cikin nasara.

A ranar Laraba ne Janar Tchiani ya jagoranci dakaru masu tsaron fadar gwamnatin ƙasar wajen tuntsurar da gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum.

Kawo yanzu tsohon shugaban na hannun dakarun na Nijar.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments