Gwamnan jihar kano Abba Kabir Yusuf ya daukaka kara akan ra,ayin kotun Sauraron Korafe korafen Zabukan Gwamna wanda ta baiwa APC dama ta kirawo wani masani Dr. Aminu Idris Harbau a matsayin Shaidarta na 32.
Abba Kabir dai ya shigar da karar ne da dalilai shida na daukaka kara, inda ya zargi cewar kotun ta yi kuskure saboda baiwa Harbau dama, bayan jam’iyar APC bata Mika bayanan sa ba a kwanaki goma bayan da aka kammala share Fagen shiga shari’ar.
Abba Kabir Yusuf ya na mai rokon kotun daukaka karar da ta rushe duk bayanan da Dr. Harbau yayi a gaban kotun inda ya ce ba,a kirawo shi bisa ƙa’ida ba.
Jaridar Kadaura24 ta rawaito cewa tuni aka sabunta bangarorin Sharia da takardun daukaka kara.
Daga yanzu zuwa kowanne lokaci, kotun sauraron daukaka kara zata sanar da lokacin da zata saurarin wannan kara da Abba Kabir Ya daukaka ya na zargin kotun sauraron korafe-korafe zaben gwamna Kano da tabka kuskure.