Gwamnatin jihar kano ta bayyana cewa ta kama tsohon kwamishinan ayyuka na gwamnatin Dacta Abdullahi Umar Ganduje, Engr Idris Wada Saleh, da karin wasu mutane biyar.
Hukumar karbar koken al’umma da kare hakkin kanawa ce ta tabbatar da kama kwamishina da wasu da wasu mukarraban ma’aikatar sa
Hukumar tace ta kama mutanen ne bisa zargin su da wawushe zanbar kudi har Naira Biliyan guda da sunan ayyukan tituna 30 da magudanan ruwa
Jaridar solace bace ta rubuto cewa ana tuhumar mutanen ne da fitar da kudin aikin da ba’a yi shi ba sam-sam