Gwamnatin tarayya zata fara karbar harajin mallakar abin hawa a kowacce shekara

Gwamnatin tarayya ta kawo tsarin biyan kudi duk shekara a matsayin shaidar mallakar abin hawa

Daga wannan N1000 da za a rika karba, ana tunanin Naira biliyan 12 zai iya shiga asusun gwamnati

Bincike ya nuna motocin da ake da su a Najeriya sun zarce miliyan 11 tun shekaru biyar da suka wuce

A tsakiyar shekarar 2018, hukumar NBS mai tattara alkaluma a kasar nan ta yi hasashen cewa akwai motoci fiye da miliyan 11.76 a Najeriya.

Bincike ya nuna a kowace shekara, ana shigo da motoci kusan 400, 000 a Najeriya. Abin da hakan yake nufi shi ne motoci sun karu sosai zuwa yanzu.

Motoci 192,287 aka shigo da su ta tashoshin kasar nan daga Junairu zuwa Oktoban 2021, a daidai wannan lokacin an shigo da motoci 114,159 a 2022.

Idan yanzu akwai motoci kusan miliyan 12.1 a tituna, kuma aka yi sa’a mafi yawancin masu amfani da su, su ka biya haraji, za a samu kudin shiga.

Sannan za a karbi wadannan kudi a hannun masu babura zuwa keke napep. Rahotanni sun fito a kan yadda gwamnati za ta mori wannan tsari.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments