Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da aka fi sani da Abba Gida Gida, ya soke karin girman da gwamnatin Ganduje ta yi wa wasu malaman makaranta a jihar
Hakan na zuwa ne bayan da wasu daga cikin malaman da abin ya shafa, suka fara sauya tsarin rayuwarsu zuwa sabon karin albashin da suka samu
Malaman sun yi kira ga gwamnan da ya dubi halin da suka tsinci kansu a ciki sakamakon matakin da ya dauka
Baya ga karin girma, an kuma karawa malaman albashi a watan Afrilu da Mayu, inda aka soke karin albashin a watan Yuni.
Wasu malaman da suka zanta da jaridar Premium Times, sun ce ba su yi tsammanin gwamnati za ta dauki irin wannan matakin ba. Wasu kuma sun ce hukuncin ya shafi lissafin da suka tsarawa kansu.