Zanga-zangar wadda ke gudana a dukkanin sassan Faransa, wannan ne karo na 9 da ke kungiyoyin kwadago ke jagorantar makamanciyarta tun daga watan Janairu.
A jiya laraba, an kai ruwa rana tsakanin jagororin fansho da shugaba Emmanuel Macron bayan da shugaban ya kafe kan kudirinsa na kari ga shekarun ritayar zuwa shekaru 64 wanda ya ce dokar za ta fara aiki a cikin shekarar nan.
Yayin ganawar kungiyoyin da shugaba Macron sun ja hankalinsa kan yadda kudirin na shi ya haddasa fushin miliyoyin Faransa, sai dai shugaban ya bayyana cewa bashi da shirin ja da baya kan dokar.
Philippe Martinez da ke jagorantar kungiyar kwadago ta CGT ya ce martani daya da za su mayarwa shugaba Macron shi ne ganin miliyoyin jama’a na zanga-zanga kuma sun kauracewa aikinsu.
Zanga-zangar ta yau alhamis ta yi mummunar illa ga bangaren sufurin Faransa ciki har da tashoshin jiragen sama da na kasa wadanda tsaya da aiki cak sakamakon yadda jami’ansu suka bi sahun masu boren.