A jiya Talata ne jagororin manyan jami’iyyun adawa a Najeriya biyu suka shigar da kara a kan neman soke sakamakon zaben shugaban kasa na watan Fabrairu da suke kalubalanta, kamar yadda takardun kotu su ka nuna, domin fara wata shari’ar da ka iya daukar tsawon watanni.
An shigar da kararraki da dama na kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasar Najeriya, amma ga dukkan alamu babu wadda ta yi nasara.
Dan takarar babbar jami’iyar adawa ta PDP Atiku Abubakar da Peter Obi na jami’iyar Labour Party, sun roki kotun daukaka kara da ta soke zaben da Bola Tinubu dan takarar jami’iyar APC ya lashe.
Shugabannin jami’iyyun adawan sun fada a wata takardar rantsuwar kotu cewa zaben na tattare da magudi kana sun zargi hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC da take doka, inda ta gaza amfani da na’urar lantarki wajen daukar sakamakon zabe daga runfunan zabe da ma wasu zargi zargin.
Atiku da Obi sun nemi umarnin kotu kan sako bayanan zaben shugaban kasa, kana INEC ta gudanar da sabon zabe.
Tinubu ya kare zaben da cewa an gudanar da shi cikin adalci.
Obi da ya shigo takara a karon farko, ya samu goyon bayan matasa da sababbin masu kada kuri’a kuma da alamar ya fadada takarar, inda ya bai wa masu zabe kwarin gwiwar samun sauyi daga shekaru na wahala da tashin hankali karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari mai shekaru 80, tsohon Janar na soja.
Amma Obi ya zo na uku bayan Tinubu da Atiku, wanda dukkaninsu nada jami’iyyu siyasa masu karfi da kuma gomman shekaru na harkokin siyasa.
APC da PDP sune suka gudanar da mulkin Najeriya tsakaninsu tun bayan karshen mulkin soja a shekarar 1999.
Masu sa ido a kan zaben sun zargi INEC da rashin cikakken shiri da kuma jinkiri wurin fara zabe amma basu yi zargin tafka magudi ba. Hukumar kanta ta roki gafara a kan matsalolin na’ura da ta fuskanta wurin kidaya.
Kotun daukaka karar tana da kwanaki 180 ta saurari karar kana ta zartar da hukunci a karar da Obi ya shigar ta kalubalantar sakamakon.