Zababben gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya ce ba ya wata tantama shi ne zai yi nasara a kotu matuƙar ‘yan adawa suka ƙalubalanci sakamakon da ya ba shi a zaɓen jihar.
Hukumar zaɓe Najeriya Inec ta ayyana Uba Sani a matsayin wanda ya lashe zaben Asabar da ta wuce, bayan ya yi galaba a kan Isa Ashiru na jam’iyyar PDP.
Zaɓen tsakanin ‘yan takarar biyu ya yi zafi sosai inda aka yi ta jan lokaci kafin sanar da sakamako.
A zantawar sa da manema labarai, Sanata Uba Sani ya ce zai yi gwamnatin sa ne tare da kowa.
Ya ce “Mun yi alkawarin za mu rike amana, mu kuma yi adalci. Za mu kuma rike kowa a daidai ba tare da mun zalunci kowa ba.”
Ya bayyana farin cikinsa kan yadda zaben ya kasance.
“Alhamdu lillahi, jama’a sun fito sun zabe ni, sun bani hadin kai, inda na yi farin ciki matuka, na san cewa an nuna min kauna a wannan zabe da aka yi.”
Game da ko ya fuskanci fargaba yayin da ake dakon sakamakon, zababben gwamnana na Kaduna ya ce na kusa da shi ne ma suka fi shi damuwa.
“Duk abin da kaga ya faru ga dan Adam, to Allah ne ya kaddari haka, domin na sha shiga zabe kuma akwai lokutan da na fadi, akwai kuma lokutan da nayi nasara.”