An bayyana Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar a matsayin mutumin da zai iya kawowa kasar nan cigaban da ya dace cikin kankanin lokaci.
Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar “Atiku Solution” ta kasa reshen jihar Kano, Eng Umar Mai Dabino ya fitar bayan kammala taron da kungiyar da gudanar a yau Lahadi 23-10-2022.
Mai Dabino yace kamata yayi mutane su dawo daga rakiyar jam’iyar mayaudara da suka jefa yan Najeriya a cikin mawuyacin hali na kunci da takura.
Taron ya Sami halartar shugabannin kungiyar daga sassan jihar Kano kuma ya gudana ne da yawun shugaban ta na kasa ENG. JANKARA