Robert Lewandowski ya ci kwallo ta 12 a wasa 11 a La Liga, bayan da Barcelona ta doke Athletic Bilbao 4-0 a ranar Lahadi a Nou Camp.
Dan wasan tawagar Poland shi ne ya ci ta uku, bayan da ya samu kwallo daga wajen Ousmane Dembele.
Tun farko Lewandowski ne ya bai wa Dembele kwallon farko da Barcelona ta fara zurawa a raga a karawar mako na 11 a gasar La Liga.
Dembele shi ne ya bai wa Sergi Roberto, wanda ya zura ta biyu a raga, haka kuma dan wasan Faransan shi ne dai ya bai wa Ferran Torres ya ci ta hudu.
Rabon da Athletic ta yi nasara a Nou Camp tun 2001/02 a wasa 20 da ta kai ziyara, inda Barca ta ci 17 da canjaras uku.
Canjaras na baya-bayan .nan da suka yi shi ne 1-1 a 2018 kuma a karkashin jagorancin Valverde a lokcin yana Barcelona inda yanzu yake jagorantar Bilbao din.