Kwamatin yakin neman zabe na Dan takarar shugaban kasa yayi martani ga gwamnoni

Sabuwar Sanarwar da ta fito daga kwamitin APC na yakin neman zaben Bola Tinubu da Kashim Shettima ta bayyana cewa ba suyi watsi da sunayen da gwamnonin jihohi suka mika masu ba.

Sakataren kwamitin takara James Falake shine ya bayyana hakan inda yace nan gaba za a sake fito da sunayen ‘yan kwamitin yakin zaben kuma yayi cikakken jawabi game da jerin ‘yan kwamitin takaran da aka fitar.

Hon. Faleke yace sunayen mutane 422 da aka saki a karshen makon da ya wuce, baya nufin an kammala fitar da sunayen ‘yan kwamitin neman zaben.

The Cable tace jawabin Faleke ya zo ne bayan ji rahotanni su na yawo wasu gwamnonin APC suna kuka a kan yadda aka yi watsi da sunayen da suka mika.

Faleke ya kara da cewa ba cikakken jerin ‘yan kwamiti aka fitar ba, akwai ragowa na nan tafe.

Rahoton Tribune yace nan gaba za a kara bada sanarwar sauran wadanda za su taimakawa takarar Bola Tinubu da Kashim Shettima a zaben da za ayi a 2023

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments