Shugaban Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano, KAROTA injiya Faisal Kabir ya jaddada Aniyar sa ta kyautata ayyukan jami’an hukumar ciki har da sake musu kaki.
Kabir ya bayyana hakan ne yayin da shugaban masu taimakawa jami’an hukumar wajen inganta aikin su wadda aka fi sani da karota mashel ya kai masa ziyara a Ofishinsa.
Injiya Faisal yace tuni suka Mika mika bukatar yiwa hukumar garambawul ga gwamna Abba Kabir kuma ya amince da yin hakan
A nasa jawabin tun da fari shugaban karota mashel yace a shirye suke suyi aiki kafada da kafada da hukumar KAROTA domin kyautata ayyukan hukumar da ci gaban al’ummar Kano