Shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya kafa kwamiti na musamman da zai kawo gyare-gyaren manufofin tattalin arziki a Najeriya.
Tashar yada labarai ta Channels TV ta ce an yi bikin kaddamar da kwamitin a fadar Aso Rock Villa da ke birnin tarayya Abuja.
Mai taimakawa Shugaban Najeriya wajen harkoki na musamman, sadarwa da dabaru, Dele Alake ne ya fitar da sanarwa hakan a ranar Talata.
Kwamitin zai zama karkashin jagorancin kwararren masani a harkar haraji da kudi kuma shugaba a Prince Water house Coopers, Taiwo Oyedele.
Taiwo Oyedele da sauran ‘yan kwamitin da aka zakulo dagaciki da wajen gwamnati za su taimaka wajen kawo dokoki da duk tsare-tsaren tattali.
Jaridar Punch ta ce kwamitin zai fito da hanyoyi tare da tsara yadda za a rika tattara haraji a Najeriya ba tare da an rika samun tufka da warwara ba.