Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya nuna gamsuwar sa ga kokarin samar da asibitin Nigeria-Libanese Hospital wanda al’ummar kasar Labanon mazauna jihar kano suka samar domin rage yawan fita kasashen waje dan neman lafiya
Hakan ya biyo bayan
wata ziyara ta gani da ido da Mai Martaba Sarkin Kano yakai sabon asibitin dake unguwar bompai dake a yankin karamar hukumar Nassarawa.
Alhaji Aminu Ado Bayero, yayi nuni da cewar asibitin zai taimakawa al’umma musamman masu tafiya kasashen waje don neman lafiyar su.
Ya kuma yaba ga wadanda suka samar da sabon asibitin.
A nasa bangaren shugaban asibitin Abbas Hajaaj yace nan gaba kadan zasu bude asibitin da kuma daukar sababbin ma’aikata da zasu kula da marasa lafiya.
Ya kara da cewa, asibitin na dauke da gadajen marasa lafiya guda 52 da kuma na’urorin gwajin cututuka na zamani tare da gurin karbar haihuwa da kwantar da jarirai marasa lafiya.
Abbas Hajaaj yace sun samar da asibitin ne domin kishin jihar Kano da suke dashi.
Daga Magatakardar yada labaran masarautar kano Abubakar Balarabe Kofar Naisa