Lauyoyi sun roki gwamnatin Kano da ta jajirce wajan bibiyar shariar Ummita
Anyi kira gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin mai girma Dacta Abdullahi Umar Ganduje da ta da ta saka ido wajan tabbatar da ganin an hukunta Dan chanan da ake zargi da kisan masoyiyar sa yar asalin jihar Kano a Najeriya mai suna Ummukulthum da aka fi Sani da Ummi ta.
Kiran ya fito ne ta bakin Barista Badamasi Sulaiman Gandu a wata Takardar mai dauke da Sa hannunsa wadda aka rabawa manema labarai.
Takardar mai dauke da kwanan wata 22-09-2022 Bayan yabawa kokarin gwamna da tayi na jajirce wa akan Shariar Hanifa Abubakar da malamin ta ya sace ta tare da kashe ta wanda gwamnati sai da taga an hukunta shi a wannan ma ta bukaci gwamnan da ya jajirce wajan ganin an karbi hakkin ran Ummita.
Gandu yace Alummar Kano suna dauke da farin cikin cewa gwamnati zata bibiyi wannan sharia har zuwa karshe domin samar da adalci ga Ummita kamar yadda suke tsammani duba da jajirce war da gwamnati tayi akan Shariar Hanifa Abubakar.