Me zai faru idan ba a warware rikicin APC da PDP nan kusa ba?
Daga Walid Hari.
A yayin da yaƙin neman zaɓukan 2023 na Najeriya ke ƙaratowa, rikici yana ci gaba da dabaibaye manyan jam’iyyun ƙasar na APC da PDP.
Tsohon sakataren gwamnatin tarayyar ƙasar Babachir Lawal ya sha alwashin APC ba ta kai labari ba saboda batun ɗan takarar shugaban ƙasa da mataimakinsa duk Musulmai ne, a ganinsa mummunan shiri ne na raba kan arewacin ƙasar.
“Ga dukkan masu son haɗin kan ƙasar nan, musamman ma na arewa inda su abin zai fi shafa, wannan tafiyar ba za ta yi nasara.
Kuma za mu tabbatar sai mun kayar da su ta yadda babu bwani mai cikakken hankalin da zai sake tunanin hakan,” in ji Lawal.
Ya ce ba shi da tsohon shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara ba ne kawai suke adawa da wannan tikiti na Musulmi da Musulmi na APC.
Lawal wanda ya faɗi waɗanan maganganun a wata hira da gidan talabijin na Arise ranar Laraba 21 ga watan Satumba, ya ce tuni sun fara gangain nuna wa mutane cewa wannan tafiya ba mai kyau ba ce.