Dan takarar Gwamna a jamiyyar PRP Alhaji Salihu Tanko Yakasai ya jaddada aniyarsa ta cigaba da Kai ziyara kananan hukumomin jiharnan 44 don sanin halin da alummomin yankunan ke ciki a fadin jihar nan.
Dan takarar ya bayyana hakan ne a zantawarsa da manema labarai a nan kano.
Alhaji Salihu Tanko Yakasai ya bayyana cewar jamiyarsu karkashin jagorancin sa sun zagaya kananan hukumomin jiharnan don ganewa idonsu halin da alummar wadannan yankunan ke ciki wanda da zarar Allah mai kowa mai komai ya basu nasara babban zaben shekara ta 2023 Zasu yi iyaka bakin kokarinsu wajen magance musu matsalolin dake addabar yankunan a fadin jihar Kano.
Ya kuma bayyana cewar wannan ziyara ta kunshi Sada zumunci da neman tubarraki ta hanyar Kai wa malamai da hakimai da dagatai da masu ungunwanni dama tsofaffin jagororin jamiyyar tun tana NEPU.
Yakasai ya kuma bayyana cewar nan bada jimawa jamiyyar zata kai ziyara mazabu dari hudu da tamanin da hudu don duba halin da yayan jamiyya da alummar su ke ciki.
Dan takarar Gwamnan ya kuma baiwa magoya bayansu dama sauran alummar jiharnan tabbacin cewar gwamnatin su zata sauko kasa don tafiya da alumma ta hanyar sauraron matsalolin su tare da ganin ta tabbata magance musu shi.
Daganan sai yayi kira ga yan takarkarinsu kan su cigaba da bashi hadin kai da goyon baya dari bisa dari wajen ganin an cimma nasarar da ake da bukata, inda yace shi Kai zai iya tafiyar da alamuran jamiyyar ba ba tare da goyon bayan su ba.
Daga karshe Sai ya bayyana farin cikinsa tare da taya daukacin alummar musulmi murnar zagayowar sabuwar shekarar musulunci inda yayi fatan Allah ya zabawa kasarnan Shugabanni nagari da kuma samun zaman Lafiya mai dorewa a fadin kasarnan.