Ma’aikatar harkokin wajen Saudi Arabia ta yi maraba da kisan da Amurka ta yiwa shugaban kungiyar al-Qaeda Ayman al-Zawahiri, wanda hukumomi suka shafe tsawon lokaci suna nema ruwa a jallo sakamakon hannunsa a kitsa harin ranar 11 ga watan Satumban 2001 ko kuma 9/11.
Sanararwar ma’aikata harkokin wajen ta Saudiyya na zuwa ne jim kadan bayan sanarwar da shugaba Joe Biden na Amurka da ke ikirarin cewa a wani samame ne da ta kai da jirgi mara matuki, Amurka ta kashe Zawahiri, daya daga cikin ‘yan ta’addan da aka fi nema ruwa a jallo a duniya.
Shugaba Joe Biden a jawabinsa na asubahin yau talata ya ce Amurka ta yi nasarar kisan jagoran ne a hare-haren da hukumar CIA kai da jiragen yaki kan maboyar mayakan na al-Qaeda da ke birnin Kabul na Afghanistan.
A cewar Joe Biden a lahadin da ta gabata ne dakarun na ta suka kaddamar da farmakin a babban birnin na Afghanistan.
Zawahiri wanda kwararren Injiniya ne ya karbi jagorancin kungiyar al-Qaeda ne a shekarar 2011, bayan mutuwar Osama bin Laden, wanda aka yi amannar tare suka kitsa harin na ranar 11 ga watan Satumban 2001 ko kuma 9/11.