Kungiyar shugabannin jam’iyyar NNPP na reshen jihohi sun bukaci Rabiu Musa Kwankwaso ya rubuta takarda cewa ya yi murabus.
Muddin ‘dan takaran shugaban kasar a zaben 2023 bai yi murabus ba, The Guardian ta ce shugabannin sun yi masa barazanar korarsa daga NNPP.
Zargin da ake yi wa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso shi ne ya yi wa jam’iyyarsa zagon-kasa tare da nada marasa gaskiya su jagoranci NWC.
Shugabannin na NNPP su na so jagoransu ya yi masu cikakken bayanin dangantakarsa da APC a lokacin zabe da bayan gama takara.