Hamɓararren shugaban kasar Nijar ya roƙi kasar Amurka da “dukkan ƙasashen duniya” da su taimaka “wajen mayar da ƙasar kan turbar mulkin dimokuradiya bayan juyin mulkin da aka yi masa a makon jiya.
Cikin wata maƙala da ya rubuta a jaridar Washington Post, Shugaba Mohamed Bazoum, ya ce ya rubuta maƙalar ce a matsayin wadda aka yi “garkuwa” da shi.
Rashin kwanciyar hankali na ƙara ta’azzara a ƙasar da ke yammacin Afrika tun bayan hambarar da shugaban.
A ranar Alhamis, shugaban da ya jagoranci juyin mulkin ya sanar da kiran jakadunsu gida daga ƙasashen Faransa da Amurka da Najeriya da kuma Togo.
Cikin sanarwar da ya yi a gidan talabijin na ƙasar hanbararren shugaban kasar Niger Muhammad Bazoum ya ce, aikin da waɗannan jakadu huɗu ke yi ya zo “ƙarshe”.
Nijar dai na ɗaya daga cikin ƙasashen da ke samar da sinadarin yuraniyom, kuma wata babbar hanya ce ga ‘yan cirani daga Arewacin Afrika da kuma Mediterranean.
A maƙalar da ya rubuta, Shugaba Bazoum, ya yi gargaɗin cewa, matuƙar aka yi nasara kan wannan juyin mulki, “to hakan zai haifar da mummunan sakamako ga ƙasarmu da yankinmu da ma duniya baki ɗaya”.
“Dole mu yi yaƙi domin kare abin da aka sammu akai, ciki har da tsarin dimokradiyya da ake zaɓe da kuma mutunta doka da oda, wanda kuma itace hanya guda da za mu samu ci gaba mai ɗorewa da yaƙi da talauci da kuma ta’addanci, ” in ji Bazoum.
“Ba za a taɓa mantawa da goyon bayan da mutanen Nijar suka nuna ba a wannan mawuyacin lokacin mai cike da tarihi. “
A ranar Alhamis, dubban mutane suka fantsama kan titunan Yamai babban birnin ƙasar, a wata zanga-zangar
zaman lafiya da ta gudana domin nuna goyon baya ga juyin mulkin.
Sun yi tir da matakin da ƙasashen Afrika ta Yamma suka ɗauka da ECOWAS na ƙaƙabawa ƙasar takunkumin kuɗi da na kasuwanci.
Bazoum, wanda shi ne shugaban Nijar na farko da ya gaji wani kan tsarin dimokraɗiyya, ya na tsare har yanzu ƙarƙashin kulawar dakarun da suka yi masa juyin mulki a makon jiya, wanda aka ayyana Janar Abdourahmane Tchiani a matsayin shugaban kasa.