Zabar Tinubu da Gawuna zai dawo farfado da kasuwancin jihar Kano: Hajiya Maryam Musa Gawuna

Kungiyar yankasuwa ta Tinubu Gawuna dake jihar kano ta Sha alwashin ci gaba da wayar da kan yankasuwa akan su shigo a dama da su domin ganin jamiyyar APC ta lashe zabuka a shekara ta 2023 Mai zuwa.

Shugabar kula da harkokin Mata ta Kungiyar Hajiya Maryam Musa Gawuna ce ta bayyana haka a ci gaba da zagayen da Kungiyar take yi a kasuwannin jihar kano domin dabbaka Alamuran Kungiyar da ma manufafinta.

Maryam ta baiwa yankasuwa tabbacin cewa Idon Tinubu da Nasuru Gawuna suka lashe zabuka za su farfado da harkokin kasuwanci da bunkasa tattalin arziki ta yadda alumma za su ji dadin Rayuwa.

Ta ce jamiyyar APC ta samu shugaban da yake ba da gudunmawa Don ganin jamiyyar ta APC ta take rawar gani wato, Baffa Babba Danagundi, inda tace jamiyyar ta yi hangen nesa bisa zabo Baffa, mutum ne mai tausayawa na kasa a kodayaushe.

Maryam tace, yanzu haka Kungiyar Tinubu Gawuna Treders Association ta zagaya kananan hukumomi Sama da goma domin tattaunawa da yankasuwa maza da Mata domin su zo a wannan tafiya domin ganin jamiyyar ta lashe zabuka a 2023.

Tace Kungiyar ba za ta gajiya ba wajen wayar da kan yankasuwa domin shigowa a dama da su a harkokin siyasa a daina barinsu a baya.

Ta Kuma bukaci Mata na gida Dana kasuwanni da su jajirce domin ci gaba da ba da gudunmawa ta yadda za a bijiro musu da tallafin Sana, oin dogaro da Kai domin tsayawa da kafafuwansu, da kaucewa Dorawa mazajensu nauye_nauyen wasu bukatu da suka fi karfinsu.
Ibrahim sani gama.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments