Sojoji sun raunata yan bindiga har maboyar su

Jami’an sojin rundunar Operation Forest Sanity sun farmaki maboyar ‘yan bindiga a kokarin da suke kakkabe dazukan Kuriga-Manini-Udawa a hanyar Chikun zuwa Birnin Gwari a jihar Kaduna.

Kwamishinan tsaron jihar Kaduna, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.

Aruwan ya ce, jami’an tsaron sun yi arba da ‘yan bindiga, kuma sun tsere da raunukan harbin bindiga yayin da sojoji suka fi karfinsu.

Sanarwar ta kuma kara da cewa, an kwato bindiga kirar AK-47, harsasai 18 da kuma wasu makamai 11. Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng! A cewar sanarwar:

“A farmakin da aka kai maboyar, rundunar tsaro ta ceto mutum uku da aka yi garkuwa dasu, sune; Luka Ibrahim, Yusuf Jibril da Saminu Abdullahi.

”Ta kuma kara da cewa, gwamnatin jihar Kaduna ta yaba da kwazon soji bisa wannan nasara da suka samu na fattakar ‘yan bindiga, haka nan Daily Sun ta ruwaito. Aruwan ya kara da cewa:

“Wadanda aka ceton tuni an hada su da ahalinsu. Dakaru za su ci gaba da aiki tukuru a dukkan yankunan.

” Hakazalika, ya kuma nemi mazauna jihar da su sanar da jami’an tsaro duk wani motsin ‘yan ta’adda ta wadannan lambobin wayar 9034000060 da 08170189999.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments