Allah yayi mahaifiyar Shugaban Hukumar KAROTA, Baffa Babba Danagundi, Rasuwa

Bayanai daga Hukumar Kula da Zirga-zirga Ababen Hawa ta jiha KAROTA na nuni da cewa mahaifiyar Shugaban Hukumar Hon Baffa Babba Ɗan’agundi Allah yayi mata rasuwa.

Ta rasu a jiya Lahadi da daddare sakamakon gajeriyar rashin lafiya

Mun sami Sanarwar da jami’in hulda da jama’a na Hukumar KAROTA Nabilisi Abubakar kofar Na’isa.

Sanarwar tace za a yi jana’izar ta a yau Litinin da misalin karfe 10 na safe a unguwar Ɗan’agundi gidan marigayi Sarkin Dawaki Babba

Muna addu’ar Allah ya jiƙanta da gafara ya sa ta huta ya bamu haƙurin jure rashin ta.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments