Zababben gwamnan jihar Kano a jam’iyar NNPP injiya Abba Kabir Yusuf ya yi alkawarin bude makarantun koyar da sana’oi da gwamnati mai barin gado tayi halin ko in kula da su ta hanyar yi musu rikon sakainar kashi
Abba Gida-gida ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi ga wasu gungun masoya magoya baya da suka ziyarce shi har gida.
Yace gwamnatin da zai karba zai tabbatar da ganin ya samar da kayayyakin koyar da sana’oi na zamani domin Inganta rayuwar mata da matasa.
A cewar sa makarantu 26 na koyar da sana’oi da Kwankwaso ya kirkira sakamakon gwamnati mai barin gado yasa suka rufe su zai tabbatar da sun dawo aiki