Yan bindigan sun yi awon gaba da kwamishinar yayin da take kan hanyar zuwa Patakwal, babban birnin jihar Ribas daga garin Brass na jihar Bayelsa
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun sace kwamishinar ne tare da Direbanta da kuma yar aikinta a kan hanyar zuwa garin Fatakwal
jaridar punch ta ruwaito cewa maharan sun sace matar, direba da mai aikinta da misalin ƙarfe 6:30 na yamma ranar Lahadi bayan ta dawo daga ƙarar hukumar Brass.
A halin yanzun wasu bayanai sun nuna cewa masu garkuwa da Misis Izonfuo sun aiko da saƙo, sun nemi miliyan N500m a matsayin kuɗin fansa.
Jami’ar hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda reshen jihar Ribas, Grace Iringe-Koko, ya tabbatar da sace kwamishinar NPC ta ƙasa.
Ya ƙara da cewa kwamishinan hukumar ‘yan sandan jihar ya tashi tawaga ta musamman kuma ya ɗora musu alhakin tabbatar da cewa wacce aka sace ta kubuta lami lafiya