Daga Walid Hari.
An yi wa kwallon da aka yi daya daga cikin fitattun wasan kofin duniya da aka yi tsakanin Ingila da Argentina a 1986 farashi da ya kai fam miliyan 3.
An sayar da kwallon ga Ali Bin Nasser dan kasar Tunisia, wanda shi ne alkalin da ya busa wasan da ya bayar da kwallon da Maradona ya ci wadda ake kira ‘Hand of God’ a wasan.
Maradona ne ya fara cin kwallo a wasan – ta hanayar naushinta kuma kwallon ta wuce mai tsaron ragar Ingila Peter Shilton.
Bin Nasser bai duba kwallon ba ya bayar da ita, yayin da dan wasan daga baya ya yi bayanin cewa “rabin kwallon ya taba kan dan wasan rabi kuma kan Maradona”.
Kwallo ta biyu da ya ci a wasan ta yi sunan da ake kiranta da “kwallon karni”,
Argentina ce ta yi nasara a wasan da ci 2-1 kuma daga karshe ta ci kofin duniyar da aka yi a Mexico.