A kwanakin baya babban sakataren majalisar dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya yi kira ga kasashen duniya da su taimakawa kasashen Africa domin su tinkari matsalar sauyin yanayi.
A yayin taron manema labarai da aka saba shiryawa a yau Alhamis, mai magana da yawun ma’aikatar harkoki wajen kasar China Mao Ning, ta bayyana cewa, kasar China nayi du mayyuwawa wajen ganin ta tallafawa kasashen Africa.
Ning tace “Mun lura da kalaman Guterres. Kuma kasar Sin tana tsayawa tsayin daka ba kuma tare da yin kasa a gwiwa ba wajen agazawa matakan da Afirka ke dauka game da matsalar sauyin yanayi.”