Daga Sani Abdulsalami Danbala
Shugaban kungiyar malaman makarantun Sakandire na kasa reshen jihar Kano Kwamared Abdu Usman Yalo ya bayyana cewa kasar nan na fatan samun Shugaban da zai bada kulawa sosai a sha,anin Ilmi.
Ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a ofishinta, yace babu shakka harkar Ilimi abu ne da yakamata shuwagabanni su bawa fifiko fiye da sauran ayyuka.
Ya kara da cewa Gwamnatin kano tayi kokari wajen inganta sha,anin Ilmi musamman tsarin maida Ilimi kyauta kuma dole da kuma samar da kayayyakin koyo da koyarwa a makarantu gami da gyara gine ginen makarantu a fadin jihar.
Kwamared Yalo yace a Shugabancinsa na wannan kungiya sun cimma nasarori da dama ciki harda Samawa malamai lamuni a bankin Samar da muhalli ga al,umma wato (Federal Mortgage Bank) a inda tuni shiri yayi nisa na Samawa malamai 500 lamuni a Bankin a kashi na farko.
Ya kara da cewa baya ga haka akwai tsari na samar da Babura lamuni wanda shima malamai da dama zasu amfana a inda shima shiri yayi nisa wajen rabon baburan.
Abdu Usman Yalo yayi kira ga malaman da su cigaba da jajurcewa wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu don cigaban Ilimi a fadin jihar kano dama kasa baki daya.