Ƙungiyar bayar da agaji ta Oxfam ta ce akwai yiwuwar yunwa za ta rinƙa hallaka mutum ɗaya a cikin kowane daƙiƙa 36 a Somalia daga yanzu zuwa ƙarshen wannan shekara.
Ƙungiyar ta ce hakan zai faru ne sanadiyyar fari da ke addabar yankin.
Yanzu haka yanki mai fadi na ƙasar Kenya, da Somalia da kuma Habasha na gab da fuskantar hari a karo na biyar a jere.
Wannan ya sanya miliyoyin mutane na baro ƙauyuka suna komawa sansanonin da ake samarwa a kusa da birane.
Oxfam ta ce yawan waɗanda tsananin yunwa ya tagayyara a Somalia yanzu haka ya zarta waɗanda lamarin ya shafa shekara 2011 lokacin da aka yi fama da yunwar da ta kashe mutum 250,000.
Yakin da ake yi a Ukraine ya ƙara ta’azzara matsalar, inda farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron-zabi.