Kotu ta soke takarar Aishatu Binani a matsayin yar takarar gwamnan jihar adamawa a Jam’iyyar APC.
Daga Walid Hari.
Babbar kotun tarayya dake zamanta a birnin Yola jihar adamawa ta soke zaben fidda gwanin dan takarar gwamna na jam’iyyar Apc da aka gudanar wanda Aishatu nai Nasara.
Kamar yadda alkalin babbar kotun ya sanar Jam’iyywar Apc bata da dan takarar gwamna a babban zaben 2023 me gabatowa, amma yace da mai kara da wanda aka kai kara sunada damar daukaka kara anan gaba.