Ministan shari’a Malami yace Kotu Ta Wanke Nnamdi Kanu Amma Bata Ce Musakeshi ba
Daga Walid Hari.
Ministan Shari’a, kuma babban lauyan gwamnati, Abubakar Malami, ya yi tsokaci kan hukuncin kotun daukaka kara da ta wanke Nnamdi Kanu, jagoran kungiyar dake rajin kafa kasar Biyafara watau IPOB.
A jawabin da mai magana da yawunsa, Dr. Umar Jibril Gwandu, ya fitar, Malami ya ce “kawai kotu ta wanke Kanu ne amma bata ce a sakeshi ba.
Saboda haka, zamu dauka matakai kuma zamu yiwa jama’a bayanai lokacin da ya kamata.
Abinda kotu ta yanke hukunci kai shine yadda aka dawo da shi Najeriya, amma a fahimci cewa akwai wasu lamuran da ake zarginsa da su kafin guduwan da yayi” Acewar Mr Malami.