Gwamnatin kasar Chadi ta ba da sanarwa a jiya Alhamis cewa, jami’an tsaron kasar, sun yi nasarar murkushe wata makarkashiya da wasu sojojin kasar suka kitsa ta hambarar da gwamnati mai ci.
Sanarwar ta ce, jami’an soja 11 ne, suka kitsa wannan makarkashiya da ta zama barazana ga tsaron kasar.
Gwamnatin Chadi ta ce, an kama wadanda suka aikata laifi, ana kuma gudanar da bincike a kan su.