Talaka ba abin yadawa bane, duba da yadda yake fadi-tashi akan yan siyasa: Gwamnan jihar Zamfara

Talaka ba abin yadawa bane,kamatuwa yayi masu rike da madafan iko na siyasa, su maida hankali Gaya wajen rungumar aluma domin Jin irin matsalolin da ke addabar sa.

Gwamnan jahar zamfara, Muhammad Bello matawallen muradun shine ya bayyana haka a yayin taron Bude babban ofishin kungiyar G7 business community da yayan kungiyar suka yi kaura irin na siyasa daga jamiyar PDP zuwa jamiyar APC karkashin jagorancin Mai girma gwamna matawallen maradun da ya gudana a shelikwatar kungiyar ta G7 dake Kan titin gidan zoo,

shi ko babban daraktan kungiyar G7 Hon Ibrahim Khalil Ahmad ya ce babu abinda ya ja raayinsu game da dawo war su jamiyar APC face karamci da gwamna zamfaran ya nuna musu Hakan ya sa su canza shekar, Kuma babu gidan da suka dauka Sai gidan matawallen saboda mutum ta Dan Adam.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments