Hukumar hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa ba tallan ya’ya mata take kalubalanta ba illah kawai daren da yammatan suke kaiwa a yayin tallan nasu.
Mataimakiyar kwamandan hukumar hisbah ta jihar kano malama kulsum kasim ce ta bayyana hakan a yayin rangadin da ta sake kaiwa wuraren tallan yammatan a sabon titin fanshekara da kuma titin gidan zoo domin dakile tallan dare da yaran suke tun daga safiya har zuwa dare.
Rangadin an gudanar dashi ne tun daga karfe bakwai na yamma zuwa takwas na dare yayin da ta bayyana cewa hukumar Hisbah bata goyon bayan su ringa kaiwa dare a talla.
Malama Rabi Bello ce ta jagoranci tawagar mata masu aikin samame tace duba da yadda tarbiyya ya’yan take cikin hadari suke samun bata gari su lalata su wasu kuma su samu ciki ta hanyar da bata daceba shine makasudin Kai ziyarar gargadin da hukumar ta Kai a wuraren da suka hadar da tashar sabon titin fanshekara da titin gidan zoo da kuma titin Ibrahim taiwo inda ya tallan suka fi dafdala.
A nata bangaren malama sadiya Bello kibiya mataimakiyar Mai kula da matan sashen samame ta CE sunyi bakin kokarinsu domin yaran su San kauna CE zallah hukumar hisbah take nuna musu amma abin ya gagara inda kuma wasu daga cikin masu sana,a a wuraren tallan yaran suka ce abin yayi musu dadi domin yaran har karfe 10:00 na dare suke kaiwa don haka suna goyan bayan hukumar hisbah.