An shawarci matasa da su kasance masu Neman sana,oin dogaro da kawunansu komai kankantarsu domin kaucewa shiga ayyukan batagari.
Shugaban kungiyar unguwar gidan kara gadar rimin kebe kuma,mai rajin ci gaban yankunan Alh Bashari Tukur ne ya ba da wannan shawarar a lokacin da yake yiwa manema labarai Karin haske akan Neman sanaoin dogaro da kai a ofishinsa dake gadar rimin kebe a karamar hukumar ungogo dake nan jihar kano.
Alh Bashari yace,kamata yayi matasa su daina raina kananan sana’oi kasancewar daga kananane suke zama babba ,Inda yace,idon matashi ya rasa sana,a babu wani Abu da zai zo zuciyarsa,sai tunani tunanin ya zai yi ya samu kudade,Wanda daga nan ne,in ba,ayi sa,a ba,zai fara roko daga hannun mutane ko ya shiga wasu ayyuka da basu kamata ba.
Shugaban yace,ba komai ne,yake janyo irin wannan ba,sai raina kananan sana,oi da wasu daga cikin matasa ke yi a lokuta daban daban,Wanda hakan ba zai haifar musu da ‘da’ mai ido ba,kuma ba zai taimakawa rayuwarsu ba.
(Alh Bashari Tukur gadar rimin kebe, yace ya tuna lokacin da ya fara sana,ar siyar da man _gyada ya farata ne da galan guda,yana nan yana gudanar da sana,arsa har Allah subahanahu wata,ala ya sa mata albarka,inda yace,yanzu haka,ya kafa kamfani nasa na Samar da man gyada da hada dusar abincin kaji da sauran abubuwa da a baya ba,a San da su ba,Wanda a halin yanzu yana da ma,aikata da suke cin abinci a karkashinsa,inda yace wannan ba karamin abin alfahari bane.)
Bashari Tukur gadar rimin kebe, ya kara da cewa,a cikin wannan sana,a ta harkar kasuwancin gyada da kuli_kuli da sauran makamantanta sa,a ce,ta iyaye da kakanni da kuma,rufin asiri,wadda in an mayar da hankali to fa,a iya samun nasara da ci gaba maigirma.
Shugaban yace,kowacce irin sana,a matashi ya dauka da mahimmanci Allah zai agaza masa a cikinta,domin duk Wanda ka gani da kudi ko arziki,in ya baka labari sai ka tausaya masa.
A don haka,yake kiran matasa da su kaucewa shiga harkokin shaye_shaye da roko,sai kuma,uwa uba kwacen wayoyin alumma,Wanda yanzu ya zama ruwan dare a tsakanin wasu daga cikin matasa, yace wannan shekara an samu kayan amfanin gona,musamman gyada da waken suya wadanda har,yanzu farashinsu ya kara tashi.
Alh Bashari Tukur, ya bukaci matasa da su kaucewa shiga bangar siyasa ko su bari wasu su yi amfani da su wajen cin mutuncin Alumma,musamman a wannan lokacin da harkokin zabe suke karatowa,inda yace,kamata yayi matasa su yi karatun ta nutsu wajen ganin sun zabi shugabanci nagari da zai tallafawa rayuwarsu anan gaba kasancewar,matasa sune shugabannin gobe.
Daga nan ya yi kira ga Gwamnatoci matakai daban_daban, da su taimakawa al,amuran matasa a fadin kasar nan,saboda rashin baiwa matasa sana,oin dogaro da kai,Ma daya daga cikin abubuwan da suke haifar da rashin cikakken tsaro a tsakanin alumma.
Yace kamata yayi Gwamnati ta bijiro da managartan tsare tsaren da za su taimakawa matasa wajen cin gashin Kansu tare da tsayawa da kafafuwansu,ba tare da sun shiga roko da kashe zukatunsu,Wanda zai iya sauyasu zuwa aikata munanan dabi’u da wasu kamata ba.
Ibrahim sani gama pyramid radio.