An gano gawarwaki akalla 68, bayan wani jirgin saman fasinja mai dauke da mutane 72, ya fadi a yankin Pokhara na tsakiyar kasar Nepal a yau Lahadi. Jami’ai sun ce ana ci gaba da aikin bincike da ceto.
Wata sanarwa da hukumar kula da sufurin jiragen sama ta kasar ta fita, ta ce jirgin ATR-72 na kamfanin jiragen sama na Yeti, ya tashi daga Kathmandu zuwa Pokhara da misalin 10:30 na safiya, inda ya rasa hanyar sadarwa da hukumar da misalin 10:50.
A cewar hukumar, fasinjoji 68 da ma’aikatan jirgi 4 ne a ciki, daga cikinsu kuma akwai ‘yan kasashen waje 15.
Ministan kula da masana’antu da ciniki na kasar Abdul Khan, ya shaidawa kamfanin dillancin labaru na Xinhua cewa, gwamnatin Nepal ta ayyana gobe Litinin a matsayin ranar makoki ta kasar. Haka kuma ta kaddamar da wani kwamiti mai mambobi 5 domin binciken musabbabin hatsarin