Yawancin mutane na rasa ransu ne sanadiyyar kusantar dabbobi Dr.abubakar sani inuwa

A wannan rana ne majalisar dinkin duniya ta ware a matsayin ranar dabbobi ta duniya to ko ta yaya ya dace a ma’amalanci dabbobin

A yayin zantawar mu da Dr.Abubakar sani inuwa babban likitan dabbobi na asibitin dake kundila dake kan titin zariya kano ya bayyana farin cikin sa da zuwan wannan rana duba da cewa su a jikin dabbobi Allah ya kaddara musu hanyar neman abinci

Dr.ya yace hakika dabbobi sun shiga rayuwar Al’umma tsindin musamman ma bangaran sarrafa su ta hanyar ci a matsayin abin dadi da amfani dasu wajan bada tsaro sannan wajan bunkasa tattalin arziki

Dabbobin suna zama musabbabin yada cututtuka ga Al’umma wadan da ke yaduwa ta hanyar iska idan akai duba da kare yana yada cutar hauka da yake dauke da ita wadda ake kira da haukan kare wannan cuta tana sanadiyyar mutuwar fiye da mutum dubu hamsin a nigeria a kididdigar da ucef ta gudanar

Dr.ya bayyana irin yadda suke karbar dabbobin da suke bukatar kulawa ta fannin inganta lafiya a kalla suka duba sama da talatin a kowacce rana.

Ya shawarci Al’ummar da suke rayuwa da dabbobi dasu dinga ziyartar asibitin dabbobi domin duba su da basu rigakafi domin kaucewa yaduwar cututtuka.

Daga karshe ya karkare da bayyana cewar akwai alaka tsakanin dan adam da dabbobi ta bangaran cututtuka dan haka ka kare dabbar ka sai kaima ka tsira da lafiyar ka

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments